XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na talatin da bakwai


Sayyed Zakzaky2

Shin iyaye da miji suna da iko a kan dukiyar mace?

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ya yi alwala sai ya ji rauni a wajen alwalar har jini ya fita, shin zai sake alwalar ne ko wanke jinin ya wadatar?

Daga Muhammad Mai kananzir Kafin Hausa, Jihar Jigawa.

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ba ma dai ko guda, domin fitar jini ba shi daga cikin abubuwan da ke warware alwala. Sai dai jini najasa ne, akwai daidai gwargwadon wanda akan yafe a salla da kuma gwargwadon da ba a yafewa. In jini ya fito daidai gwargwadon wanda ake yafe shi a salla, wanda shi ne bai kai fadin dirhamin alfadari ba, to ba ma ya bukatar ya wanke.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, nine na gabatar da sallar azahar kafin in yi la'asar, sai kaikayi ya kama ni a hannu, sai na yi ta susar hannun har ya yi fari. Shin kafin na yi salla sai na sake alwala ko kuwa?

Daga Muhammad Mai kananzir Kafin Hausa, Jihar Jigawa

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai susa ba shi daga cikin abubuwan da ke warware alwala. Ko ya yi fari, ko ya yi ja, ko ya yi baki; duk daya ne.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sana'ata sai da dabbobi, sai na zuba a mota zan kai wani gari domin sayarwa. To ana cikin tafiya sai wata za ta mutu. Ganin haka sai na yanka ba tare da na kalli alkibla ba. Shin yankan ya yi ko kuwa?

Daga Muhammad Mai kananzir Kafin Hausa, Jihar Jigawa.

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, ya yi, sai dai ba a bi ladabi ba. Shi duban alkibla yana cikin ladubban yanka. Saboda haka idan wata lalura ta sa ba a kalli alkiblar ba, ba za a ce yankan bai yi ba.

TAMBAYA: Akramakallah, shin ya halasta mutum ya yi irin kiwon nan na tsuntsu, ya tsare shi a keji, kamar aku da kanari da sauransu?

Daga Aminu Imam Muhammad, 064 241140, Wudil, Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, ba abin da ya hana shi ya yi, matukar zai kiyaye da hakkin abin da yake kiwo din. In kuma ya tauye masa hakki, to lallai ya yi laifi. Kamar ya tsare shi bai ba shi abubuwan da shi (tsuntsun) zai bukata a rayuwa ba. Wala'alla ma wadansu daga cikin wadannan abubuwan da ya ambata, ko da an sake su a keji din, ya zama in sun fita za su je su dawo, ka ga sun riga sun aminta da wurin zaman nasu kenan saboda suna jin dadin zaman.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne yana da dukiya kuma ta kai misalin a fitar mata da zakka, amma ba ya fitarwa. Sai aka yi masa nasiha kuma ya yarda zai fitar. Shin zai fitar da na shekarun da suka gabata ne, ko daga wannan lokacin ne zai fara fitarwa?

Daga Haladu Abdu, Babban Asibitin Buni Yadi, Jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai duk zakkokin da suka hau kansa, matukar yana musulmi, akili, baligi, to lallai suna nan a kansa, ko da sun shekara nawa ne. Saboda haka wajibinsa shi ne ya fitar da duk na shekarun baya. Wato zai yi la'akari da duk yadda ta kama masa, bara nawa ya hau kansa? Bara waccan nawa ya hau kansa, da sauransu. Wato zai fitar da irin abin da ya hau kansa ne. Har ma inda dukiyar da ya hau ya amfana da su, har da su abin da suka hau din, duk zai bayar a matsayin zakka.

TAMBAYA: Akramakallah. An ce mace idan tana salla ba ta bayyana karatu a wurin bayyanawa, to idan ta manta ta bayyana fa? Kuma za ta iya bayyanawa idan a dakinta ne ita da mijinta?

Daga Haladu Abdu, Babban Asibitin Buni Yadi, Jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: To, idan ta bayyana bisa kuskure, babu komai. Wannan hukuncin ma haka yake ko da ga namiji ne. A inda aka ce a boye karatu, in ya bayyana da kuskure ko da mantuwa, shi ma babu komai. Haka zalika in ya asirta inda ya kamata ya bayyana. Dangane da ita kuma mace, tana iya yin karatu ta bayyana muryarta a wurin bayyanawa in wani ajanabi ba zai saurare ta ba, kamar inda ya ce a dakinta ne, in mijinta ko 'ya'yanta ko muharramanta za su saurare ta, babu komai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin wanda ya kewaya Alkur'ani don an yi masa sata da nufin Allah ya kashe wanda ya yi masa satar, ko ya hadu da wani bala'i?

Daga Haladu Abdu, Babban Asibitin Buni Yadi, Jihar Yobe

SHAIKH ZAKZAKY: To, wannan ba a san shi ba a shari'a. Ba a san cewa idan an yi sata ana yin wani abu ne da Alkur'ani don mutum ya mutu ko wani bala'i ya same shi ba. Saboda haka tana iya yiwuwa wadansu irin tsaface-tsaface ne ko tsubbace-tsubbace, wadanda da ma can Maguzawa ke yi da wadansu itatuwa, yanzu kuma wasu suke neman su yi shi da Alkur'ani. Amma ba a san shi ba a addini, kuma ba zai zama ya halatta ba.

TAMBAYA: Akramakallah, menene hukuncin dan uwan da ba ya salla a masallacin kusa da gidansa saboda su ba mabiya Imamiyya bane?

Daga Muhammad Awwal, Jos

SHAIKH ZAKZAKY: To, in ba su munana masa zato a kan cewa ba ya salla, babu komai. In kuma za su munana masa zato a kan cewa shi ba ya yin salla ne, to sai ya rika yin salla da su.

TAMBAYA: Malam ya taba cewa miji da iyaye ba su da iko a kan dukiyar mace, alhali ga hadisi ya ce mace ba ta da ikon ta yi tasarrufi da dukiyarta sai da izinin mijinta, ina neman karin bayani.

Daga Muhammad Awwal, Jos

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ni ma ina neman karin bayani dangane da ina na fadi wancan Magana. Tana iya yiwuwa wata magana ce ya dauko daga cikin wata magana ta daban, bai kawo bayaninta cikakke ba. Amma dai abin sani shi ne, ita mace tana da ikon tasarrufi a kan dukiyarta ba tare da izinin mijinta ba, sai a wadansu abubuwa kadan. Alal misali a cikin abubuwan da yake amfana da shi na yau da kullum wanda aka saya kila da sadakinta, kamar misali a ce Firij ko murhun girki ko gado ko abin da ya yi kama da haka, in ta ce ta sayar ko ta kyautar, yana iya musanta mata. Haka kuma idan wani abu ne babba kamar gida ko mota ko gona, in ya kai sulusin abin da ta mallaka, shi ma yana iya musanta mata. Amma a sauran abin da ba wadannan da muka ambata ba, tana da ikon tasarrufi a dukiyarta. Kuma ban san a ina ne aka yi batun cewa iyaye da miji ba su da iko a kan dukiyar mace ba. Ban san inda na fadi wannan ba. Illa iyaka wannan maganar tasarrufi din shi ne aka sani.

TAMBAYA: Mutane biyu ne suke kwance a daki lokacin watan azumi, sai suka makara yin sahur. Da suka tashi suka ga karfe 6:00ns ta yi, sai daya ya ci abinci, shi kuma dayan da ya ga shida ta yi, sai ya ki ci, to yaya matsayin azuminsu?

Daga Muhammad Sani Rigasa, Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY:To idan alfijir na ketowa kafin shida na safe, kuma an san haka, duk cikarsu sun sani, kamar shi wanda ya ci abincin ma ya sani cewa alfijir ya keto, in dai har ya ga 6:00 na safe, to ramuwa da kaffara ya hau kansa. Idan kuwa shi wanda ya ci abincin a zatonsa karfe 6:00 alfijir bai keto ba, sai ta bayyyana masa ashe ya keto, shi ramuwa ne kawai ya hau kansa ban da kaffara. Shi kuwa wanda da ma bai ci abinci ba, shi kenan, da ma ba wani abu dangane da shi tunda da ma bai yi sahur din ba.

TAMBAYA: Akramakallah, mutum ne bai da lafiya sai aka tashe shi don ya yi sahur, amma rashin lafiyar ta hana shi tashi da wuri. Bayan ya tashi yana cikin cin abinci sai ya ji ana ta sallar asubahi, to yaya azuminsa?

Daga Muhammad Sani Rigasa Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To, in ya kaddara cewa lokacin da ya tashi din ya dauka cewa alfijir bai keto bane, sai ya ci abinci da nufin yana sahur, to sai ya ji cewa ashe ga shi can ana salla, wato ma'ana alfijir har ya keto, to sai ya yanke cin abincin kuma ramuwa ta hau kansa, ban da kaffara. Amma in ko lokacin da ya fara cin abincin ya tabbatar da ma lallai afijr ya keto ya dai ga daman ya ci ne saboda yana ganin bai iya tashi da wuri ya ci, to shi kuma ramuwa da kaffara ne ya hau kansa. Abin da dai za a la'akari da shi shi ne, alfijir ya keto ko bai keto ba, ka sani ko ba ka sani ba? In kana tsammanin alfijir bai keto ba, sai ka ci abinci, sai ta bayyana ashe ya keto, to ramuwa ya hau kanka. Idan kuwa ka san alfijir ya keto ka ci abinci, to ramuwa da kaffara ne, tunda ka yi da gangan, kamar wanda ya ci da rana ne.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina hukuncin ruwan da aka zuba a roba don yin wankan janaba, alhali a wajen wankan, ruwan na komawa cikin na robar?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To ai ba inda aka ce ruwan da ka yi wanka da shi ba zai yiwu ka sake yin wanka da shi ba. Bilhasali ma in robar babba ce, yana iya shiga cikin robar ma ya yi wankansa na janaba din. In ma ya fito, in am akwai wadansu da za su yi wankan duka, suna iya shisshiga duk ma su yi ta yin wankan da shi. Wato ruwan da aka wanke janaba da shi, shi bai zama najasa ba ballantana ya hana a sake yin wani wankan janaba da shi. Ruwan da aka wanke bayan gida ne da shi, wato ka kama ruwa ka wanke bayan gida, shi ne wannan ba zai yi wu a yi mafani da shi wajen yin alwala ko wanka ba. Amma ba wanda ya wanke jikinsa don da janaba, sai kuma ruwan ya zama ya najastu ba. Lallai yana nan da tsarkinsa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, menene hukuncin cin naman gafiya, bushiya, damo, kurege, guza da sauran ire-irensu?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu, jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To, duk haramun ne. Ba makaruhi ba kamar yadda ya shahara a wajen amawa. Wai har suna cewa wai karahiyya, to lallai ya wuce nan. In ma karhanci ne, sai mu ce karhancin haramci ne. Haka zalika kuma duk nau'o'in beraye gaba daya, har da beran Misra da zomo, duk cin su haramun ne. Haka kuma duk abin da ke jan ciki, wanda hada da dangin su damo da guza, wanda ya hada har da su kadangare da kado da ma duk abu mai jan ciki, har da macizai, duk sun haramta a ci.

TAMBAYA: Akramakallah, na yi sammako don zuwa wani gari tun kafin lokacin sallar asubahi, don haka ne kawai zai sa na riski abin da ya kai ni. To kafin na karaisa garin, sai rana ta fito. Shin zan yi salla a mota ne ko zan bari sai na sauka?

Daga Husain Muhammad D. Almajirai Tsakuwa Dawakin Kudu, jihar Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Mai tambayar ga dukkan alamu ya jahilci lokacin salla, tun da ya dauka cewa ana yin sallar subahi ne in rana ta fito. To in alfijir ne ya keto ake yin sallar subahi. Saboda haka in ya fita gida kafin ketowar alfijir, to bayan ketowar alfijir kafin gari ya dan wattsake daidai gwargwadon abin da aka dauka lokacin sallar subahi ne, lokacin da ya fi kyau a yi, wanda a ibarar ama takan ce masa mukhtari, to mu kuma mukan ce masa lokacin Fadila. To lallai a wannan lokacin zai sauko daga motar ne ya yi sallarsa. In kuma har ma bai sauko ba, to yana da lokaci har ya zuwa wattsakewa mabayyani, kafin ketowar rana, dole ya sauko ya yi salla. In kuwa har ya bari rana ta fito, to ya yi laifi, ya aikata haramun, ya bar wajibi. Saboda haka yanzu ramuwa ta kama shi, amma kuma ya yi zunubi mai yawa.

TAMBAYA: Akramakallahu. Yaya zan yi da cin nama idan na sami kaina a Ingila ko Amerika?

Daga Muhammad M.Mustafa Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: To, alhamdu lillahi, ina jin shi wannan bai je Ingila ko Amerikan bane. In ya je zai ga ba shi da wata matsala da nama, insha Allahu. Saboda akwai musulmi a wadannan wuraren, kuma akwai nama na halas. Har ma akwai kantunan da ake sayar da naman halal. Za ka ga ma an rubuta HALAL balo-balo, har ma a gidajen cin abinci ma akwai na halal. Saboda haka in dai batun nama ne, ba shi da mishkila a yanzu duniyar nan da mike ciki a kasashe, saboda ko'ina akwai musulmi. Sai dai in ba wajen musulmi bane, wanda suka tabbatar masa da halascinsa, to ba zai ci naman ba kenan sam-sam, ko ma abin da ya fito daga nama.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ya taba yin bayani kan karin gashi ga 'ya mace, saboda haka nake neman karin bayani?

Daga Muhammad M. Mustafa Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: Tunda na taba yin bayani, saboda haka insha Allahu wancan bayanin ma, ai sai ya je ya duba da kyau.Wala'alla abin sani shi ne, wannan dai halas ne. Ba kamar yadda ama take cewa shi ne 'wasila walmustausila ba'. Domin wasila walmistausila yana da wata ma'ana, wanda yake shi ne sahihi, cewa ita ce kawaliya, wadda take sadar da mazinaci da mazinaciya. To wasila ita ce wannan kawaliya din, mustausila kuwa ita ce wadda aka sada ta da mazinacin, ba wai mai sada gashi ba. Kuma shi sada gashi ba wani abin da aka ruwaito dangane da shi. Ba a ruwaito haramcinsa ba. Saboda haka ya halatta tunda ba a sami haramcinsa ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din